Jami’ar BUK za ta gwangwaje ma’aikata da dalibanta da kayan tallafi


  • Jami’ar Bayero dake Kano (BUK) ta shirya tallafawa ma’aikata da ɗalibanta a dalilin tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasa
  • Jami’ar za ta yi rabon kayan tallafi ga ma’aikata domin rage musu raɗaɗin da ake ciki a dalilin cire tallafin man fetur da aka yi
  • Hukumar jami’ar za ta kuma samar da motocin da za su riƙa jigilar ɗalibai cikin farashi mai rahusa domin sauƙaƙa musu rayuwa

Jihar KanoHukumar jami’ar Bayero dake Kano (BUK) ta shirya gudanar da rabon tallafi ga ma’aikata da ɗalibai domin rage raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita a Najeriya.

Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas, shine ya bayyana hakan a wurin taron jami’ar karo na 56 a ranar Asabar, 22 ga watan Yulin 2023, cewar rahoton Premium Times.

Jami’ar BUK za ta saukaka rayuwa ga ma’aikata da dalibanta
Hoto: Buk.edu.ng
Asali: UGC

Kakakin jami’ar, Lamara Garba ya sake tabbatar da hakan ga wakilin jaridar a ranar Lahadi, 23 ga watan Yulin 2023.

Garba ya bayyana cewa jami’ar ta cire biyan kuɗin wutan lantarki da ruwa ga ma’aikata 500 da su ke zama a rukunin gidajen jami’ar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa ba a cire musu biyan kuɗin hayar ba ne saboda kai tsaye ake biyan kuɗin zuwa asusun ma’aikatar ilmi ta tarayya.

Rabon tallafin da jami’ar BUK za ta yi

Shugaban jami’ar ya bayyana cewa an ware wasu miliyoyin naira domin siyo kayan abinci domin rabawa ga ma’aikatan jami’ar ba tare da biyan kuɗin ruwa ba inda za su biya cikin wata shida.

Ya kuma bayyana cewa ƙaramin bankin jami’ar zai samar da bashi mara ruwa ga ma’aikata domin su samu damar biyan kuɗin makarantar yaransu.

Dangane da ɗalibai kuma, Farfesa Abbas ya bayyana cewa ana shirye-shiryen cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar Kano domin samar da motocin jigilar ɗalibai, rahoton PRNigeria ya tabbaatar.

Ya bayyana cewa motocin za su riƙa jigilar ɗalibai akan farashi mai rahusa.

Tsohon Shugaban NUC Ya Bayyana Dalilin Zabar Dawowa BUK

Rahoto a baya ya zo cewa tsohon shugaban hukumar NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya bayyana yadda ya ƙi ksrɓar tayin N20m daga wata jami’a saboda yana son dawowa BUK.

Farfesa Rasheed wanda ya ajiye aikinsa yana da sauran shekara uku ya bayyana cewa burinsa shi ne ya koma aji a BUK ya ci gaba da karantarwa.

Asali: Legit.ng

!function (f, b, e, v, n, t, s) {
if (f.fbq) {
return;
}
n = f.fbq = function () {
n.callMethod ?
n.callMethod.apply(n, arguments) : n.queue.push(arguments);
};
if (!f._fbq) {
f._fbq = n;
}
n.push = n;
n.loaded = !0;
n.version = ‘2.0’;
n.queue = [];
t = b.createElement(e);
t.async = !0;
t.src = v;
s = b.getElementsByTagName(e)[0];
s.parentNode.insertBefore(t, s);
}(window, document, ‘script’,
‘https://connect.facebook.net/en_US/fbevents.js’);
fbq(‘init’, ‘1691063087928925’);
fbq(‘track’, ‘PageView’);

if (!window.fbAsyncInit) {
window.fbAsyncInit = function () {
FB.init({
appId: ‘377376682297498’,
xfbml: true,
version: ‘v8.0’
});
};
}

(function (d, s, id) {
var js, fjs = d.getElementsByTagName(s)[0];
if (d.getElementById(id)) {
return;
}
js = d.createElement(s);
js.id = id;
js.async = !0;
js.src = “https://connect.facebook.net/en_US/sdk.js”;
fjs.parentNode.insertBefore(js, fjs);
}(document, ‘script’, ‘facebook-jssdk’));



Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *